Numbers 6:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتِ يَمِيڧَ ڟُنْڟُ طَيَ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ، طَيَنْ كُمَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا؞ تَهَكَ ذَاعَيِ هَدَايَ تَطَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ دُواْمِنْ مُتُمِنْ، غَمَا يَا ڧَظَنْتُ تَوُرِنْ غَاوَا عَثِكِنْ لُواْكَثِنْ كٜىٰٻٜىٰوَرْسَ؞ أَ رَانَرْ نَنْ ذَيْسَاكٜىٰ كٜىٰٻٜىٰ غَاشِنْ كَنْسَ دَ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.