Numbers 6:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمِنْ ذَيْسَاكٜىٰ كٜىٰٻٜىٰ كَنْسَ غَ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ يَثِكَ ݣُونَكِنْ ضَنْڟُوَارْ كٜىٰٻٜىٰوَرْسَ؞ ذَيْ كُمَ كَٰوُاْ طَنْ ضَغُواْ مَيْ شٜىٰكَرَا طَيَ دُواْمِنْ هَدَايَ تَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے؞ بَذَاعَ ڧِرْغَ لُواْكَثِنْ دَ يَيِ كَاڢِنْ يَڧَظَنْتُ دَ غَاوَا بَ، غَمَا كَيْ نَاسَ وَنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ يَڧَظَنْتُ عَثِكِنْ لُواْكَثِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.