Numbers 6:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَمِيڧَوَ يَهْوٜىٰهْ هَدَايَرْسَ، وَتُواْ طَنْ ضَغُواْ طَيَ مَيْ شٜىٰكَرَا طَيَ مَرَرْ تَبُواْ دُواْمِنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دَ یَرْ تُنْكِيَ طَيَ مَيْ شٜىٰكَرَا طَيَ مَرَرْ تَبُواْ دُواْمِنْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ دَ ضَغُواْ طَيَ مَرَرْ تَبُواْ دُواْمِنْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama,