Numbers 6:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً ڢِرِسْتِ ذَيْ مِيڧَسُ هَدَايَ تَطَغَوَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ، غَمَا أَنْكٜىٰٻٜىٰ وَنَّنْ رَبُواْ دَ ڟَرْكِے دُواْمِنْ ڢِرِسْتِ، تَرٜىٰدَ ڧِرْجِ دَ ثِنْيَ نَضَغُوانْ هَدَايَ تَطَغَوَ؞ بَايَنْ وَنَّنْ مُتُمِنْ دَ يَيِ ضَنْڟُوَارْ كٜىٰٻٜىٰ كَنْسَ، وَتُواْ نَظِرِتْ، غَ يَهْوٜىٰهْ يَنَ عِيَ شَنْ ضُوً إِنَبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi.