Numbers 6:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُكَنْ ݣُونَكِنْدَ يَطَوْكِ ضَنْڟُوَا ذَيْ كٜىٰٻٜىٰ كَنْسَ، بَذَاعَ أَسْكٜىٰ كَنْسَ بَ، ذَيْ بَرْ غَاشِنْ كَنْ يَيِ تَغِرْمَ، سَيْ ݣُونَكِنْ كٜىٰٻٜىٰوَرْسَ سُنْثِكَ، غَمَا يَا كٜىٰٻٜىٰ كَنْسَ دَ ڟَرْكِے غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A dukan kwanakin wa'adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.