Numbers 8:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ عَثِكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا نَوَنٜىٰ، كُواْ نَطَنْ أَدَمْ كُواْ نَدَبَّ؞ أَ رَانَرْدَ نَكَشٜىٰ یَیَنْ ڢَارِ نَڧَسَرْ مَصَرْ، نَكٜىٰٻٜىٰسُ وَكَيْنَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa, na mutum, da na dabba.