Numbers 8:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ حَكَ، لَوِيَاوَنْ سُكَ شِغَ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ دُواْمِنْ سُيِ عَيْكِ عَڧَرْڧَشِنْ هَٰرُونَ دَ یَیَنْسَ مَظَا، بِسَغَ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْثِ مُوسَٰى غَمٜىٰدَ لَوِيَاوَا؞ حَكَ كُوَ سُكَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da 'ya'yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.