Numbers 9:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ لُواْكَثِنْ دَ ڧُنْشِنْ غِرْغِجٜىٰ يَتَاشِ دَغَ تٜىٰنْتِنْ، جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاسُتَاشِ دَغَ ذَنْغُوانْ؞ أَ دُكْ عِنْدَ ڧُنْشِنْ يَڟَيَ، أَوُرِنْ نٜىٰ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاسُ كَڢَ ذَنْغُوانْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango.