Obadiah 1:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ كِنْجَا بَايَ دَغَ یَنْعُوَنْكِ، دَ بَاڧِ سُكَ شِغَ ڧُواْڢُواْڢِنْسُ؞ كٜىٰ عٜىٰدُوامْ، كِنْ ذَمَ كَمَرْ طَيَ دَغَ ثِكِنْ أَبُواْكَنْ غَابَا سَعَدَّ سُكَ ݣُوشِ أَرْزِڧِنْ عُرُوشَلِيمَ سُكَ كُمَ جٜىٰڢَ ڧُرِعَ عَكَنْسُ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ranan nan ka tsaya kawai, A ranar da abokan gāba suka fasa ƙofofinsa. Suka kwashe dukiyarsa, Suka jefa kuri'a a kan Urushalima. Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.