Obadiah 1:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَ دَيْدَيْ بَنٜىٰ، كِكَ شِغَ بِرْنِنْ مُتَنٜىٰنَ إِسْرَٰٓءِيلَ، كِكَ ݣُوشِ كَايَ أَ لُواْكَثِنْ مَسِيڢَرْسُ؞ لَلَّيْ بَدَيْدَيْ بَنٜىٰ، كِكَيِ مُرْنَ أَ رَانَرْ مَسِيڢَرْسُ؞ بَدَيْدَيْ بَنٜىٰ، كِكَ ݣُوشِ كَايَنْسُ أَ رَانَرْ وَهَلَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba daidai ba ne ka shiga ƙofar jama'ata A ranar da suke shan masifa. Ba daidai ba ne ka yi murna A kan bala'in ɗan'uwanka. Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsa A ranar masifarsa.