Obadiah 1:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka; abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki; waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, amma ba za ki gane ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ أَلْعُمَّنْ دَ كُكَيِ حَطِنْ ڠُوِوَ، ذَاسُ جُويَا مِكِ بَايَ؞ ذَاسُ كُواْرٜىٰكِ حَرْ كَنْ إِيَاكَرْ ڧَسَرْكِے؞ أَبُواْكَنْكِ دَ كِكَڢِے يَرْدَ دَسُو، سُنْ رُوطٜىٰكِ سُنْثِنْيٜىٰكِ دَ يَاڧِ، وَطَنْدَ سُكَثِ عَبِنْثِ دَكٜىٰ، سُنْ كَڢَ مِكِ تَرْكُواْ سُنَ ثٜىٰوَ ‹إِنَ دُكَنْ وَيُواْنَّنْ نَاتَ؟› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda kake amana da su, Za su kore ka daga ƙasarka. Mutanen da suke amana da kai, Za su yaudare ka, Su ci ka da yaƙi. Abokan nan naka da kake ci tare da su za su kafa maka tarko, Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayon nan nasa?’ ”