Philippians 4:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَيِ ڢَضٍ ثِكِ سُواْسَيْ غَ عُبَنْغِجِ سَبُواْدَ يَنْذُ كُنْ سَاكٜىٰ نُونَ كُنَ كُلَ دَنِے؞ كُواْدَيَكٜىٰ دَا مَا كُنْ كُلَ دَنِے، عَمَّا بَكُ سَامِ دَامَ كُنُونَ مِنِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba.