Proverbs 27:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كَيَاشٜىٰ أَبُواْكِنْكَ كُواْ أَبُواْكِنْ بَابَنْكَ؞ كَدَ كُمَ كَتَڢِے غِدَنْ طَنْعُوَنْكَ أَ رَانَرْ دَ مَسِيڢَ تَڢَاطَ مَكَ؞ ڠُومَّ مَڨُوبْثِ نَكُسَ، دَ طَنْعُوَ وَنْدَ يَكٜىٰ نٜىٰسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ka manta da abokanka, ko abokan mahaifinka. Idan kana shan wahala kada ka nemi taimako wurin ɗan'uwanka. Maƙwabci na kusa yana iya taimakonka fiye da ɗan'uwan da yake nesa.