Proverbs 28:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَسَا مَيْ غَسْكِيَ أَ ظُوثِ يَبِے حَنْيَرْ مُغُنْتَا، شِ دَ كَنْسَ ذَيْ ڢَاطَ ثِكِنْ رَامِنْ، عَمَّا مَرَرْ لَيْڢِے ذَيْسَامِ غَادُواْ مَيْݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan ka yaudari mutumin kirki don ya faɗa cikin mugunta, kai kanka ne za ka fāɗa cikin tarkon da ka haƙa. Marar laifi kuwa zai sami babban sakamako.