Proverbs 6:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَݣَويْ أَبُبُوَ شِدَ وَنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَڧِ، عِ، حَرْ بَݣَويْ دَ سُكٜىٰ ذَمَ مَسَ أَبِنْ ڨَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba, duban raini, harshe mai faɗar ƙarya, hannuwan da suke kashe marasa laifi, kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru, mutum mai gaggawar aikata mugunta, mai yawan shaidar zur, mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.