Psalms 13:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَرْ يَوْشٜىٰ ذَنْ جِمْرٜىٰ دَ وَهَلَرْ نَنْ، إِنْ ثِكَ دَ دَامُوَ أَ رَيْنَ دُكَنْ يِنِ؟ حَرْ يَوْشٜىٰ ذَاعَ بَرْ مَاسُ ڧِينَ سُيِ نَصَرَا عَكَيْنَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har yaushe raina zai jure da shan wahala? Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana? Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?