Psalms 139:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ دُهُ مَا أَغَرٜىٰكَ بَ دُهُ بَنٜىٰ، دَرٜىٰ كُوَ يَنَدَ حَصْكٜىٰ كَمَرْ رَانَ، دُهُ دَ حَصْكٜىٰ دُكْ طَيَ نٜىٰ أَغَرٜىٰكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka, Dare kuwa haskensa kamar na rana ne. Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.