Psalms 141:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ ذُوثِيَاتَ تَجُويَا غَ مَغَنَرْ مُغُنْتَا، كُواْ غَ عَيْكَتَ أَيُّكَنْ مُغُنْتَا تَرٜىٰدَ مُوغَيٜىٰ، كُواْمٜىٰ دَاطِنْ عَبِنْثِنْ بِكِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka tsare ni daga son yin mugunta, Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu, Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!