Psalms 144:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ یَیَنْمُ مَظَا ثِكِنْ ڧُرُثِيَرْسُ سُيِ غِرْمَ دَ ڧَرْڢِے كَمَرْ عِتَتُوَ مَاسُ لَاڢِيَ، یَیَنْمُ مَتَ كُمَ سُذَمَ كَمَرْ غِنْشِڧَنْ أَدُواْ وَطَنْدَ عَكَ سَسَّڧَ دُواْمِنْ غِنِنْ غِدَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka sa 'ya'yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka, Su zama kamar itatuwan da yake girma da ƙarfi. Ka sa 'ya'yanmu mata Su zama kamar al'amudai, Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.