Psalms 15:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنْدَ بَايَ بَادَ بَاشِ دُوانْ رِيبَ، بَايَ كَرْٻَرْ ثِنْ حَنْثِ دُواْمِنْ يَبَادَ شَيْدَرْ ڧَضْيَا عَكَنْ مَرَرْ لَيْڢِے؞ مَيْ يِنْ وَطَنَّنْ بَايَ تَٻَ جِجِّغُوَ، سَمْ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.