Psalms 22:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڧَرْڢِنَ يَڧَارٜىٰ، يَرَبُ دَنِے كَمَرْ ضُوَنْدَ يَظُبٜىٰ؞ دُكْ ڧَسُسُوَنَ سُنْ بَرْ وُرِنْ ذَمَنْسُ؞ كَمَرْ كَكِنْ ظُمَنْدَ يَنَرْكٜىٰ، ڧَرْڢِنْ ذُوثِيَاتَ يَبَرْ نِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙarfina ya ƙare, Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa. Dukan gaɓoɓina sun guggulle, Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.