Psalms 25:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَغَرٜىٰكَ، يَا اللَّهْ نَا، نَكٜىٰ دُواْغَضَ؞ كَدَ كَبَرْ نِے إِنْ شَا كُنْيَا، كَدَ كَبَرْ مَاسُ ڧِينَ سُيِ مِنِ دُوبَنْ رٜىٰنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A gare ka nake dogara, ya Allah. Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa, Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!