Psalms 27:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبُ طَيَ نَكٜىٰ ضُواْڧُواْ أَوُرِنْ يَهْوٜىٰهْ ، أَبُ غُدَا تَكْ نَكٜىٰ نٜىٰمَ، شِينٜىٰ إِنْ ذَوْنَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ دُكَنْ ݣُونَكِنْ رَيْنَ، إِنْيِ تَجِنْ دَاطِنْ غَنِنْ دَرَجَرْسَ، إِنْكُمَ نٜىٰمِ نُڢِنْسَ عَثِكِنْ هَيْكَلِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji, Abu ɗaya kaɗai nake bukata, Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji, In yi ta al'ajabin alherinsa Dukan kwanakin raina, In roƙi biyarwarsa a can.