Psalms 28:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، أَغَرٜىٰكَ نَكٜىٰ كِرَا! جِ كُوكَنَ، يَا دُوڟٜىٰنْ ٻُيَنَ! عِدَنْ كَا يِشِضُ، ذَنْ ذَمَ كَمَرْ مَاسُ غَنْ‌غَرَ ذُوَا رَامِنْ مَتَتُّو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni, Ka ji kukana! In kuwa ba ka amsa mini ba, Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.