Psalms 37:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَا ذُوثِيَارْكَ غَ يَهْوٜىٰهْ كَكُمَ كَسَنْثٜىٰ أَ حَنْيَرْسَ، ذَيْ طَوْكَكَاكَ كَثِ غَادُوانْ ڧَسَرْ، سَعَدَّ أَنْكَوَرْدَ مُوغَيٜىٰ، ذَاكَ غَنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka sa zuciyarka ga Ubangiji Ka kiyaye dokokinsa, Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar, Za ka kuwa ga an kori mugaye.