Psalms 40:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَسَ سَابُوَرْ وَاڧَا عَبَاكِنَ، وَاڧَرْ يَبُواْ غَ اللَّهْ نْمُ؞ مُتَنٜىٰ دَيَوَ ذَاسُ غَ وَنَّنْ، سُجِڟُواْرُواْ، سُكُمَ دُواْغَضَ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya koya mini raira sabuwar waƙa, Waƙar yabon Allahnmu. Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata, Za su kuwa dogara ga Ubangiji.