Psalms 40:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَا، أَيُّكَنْكَ نَبَنْ مَامَاكِ سُنَدَ يَوَ! شِرْيٜىٰ شِرْيٜىٰنْكَ غَرٜىٰمُ سُنْڢِے غَبَنْ ڧِرْغٜىٰ! كُواْ دَ نَسُواْ إِنْيِ شٜىٰلَرْسُ، كُواْ إِنْ بَادَ لَابَرِنْسُ، يَوَنْسُ سُنْڢِے غَبَنْ ڧِرْغٜىٰ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna. Ba wani kamarka! Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka, Sun fi ƙarfin in faɗa.