Psalms 43:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا اللَّهْ ، نُونَ رَشِنْ لَيْڢِينَ، كَكُمَ نٜىٰمَ مِنِ حَكِّنَ دَغَ أَلْعُمَّيْ مَرَسَ حَلِنْكَ؞ ثٜىٰثٜىٰنِ دَغَ مَاسُ رُوطُ دَ مَاسُ ثُوتَا!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya Allah, ka kuɓutar da ni, Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka, Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!