Psalms 57:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَاسُ ڧِينَ سُنْسَا مِنِ تَرْكُواْ، دَامُوَ تَشَا ڧَرْڢِنْ رَيْنَ؞ سُنْ حَڧَ رَامِ عَكَنْ حَنْيَتَ عَمَّا سُو دَكَنْسُ سُكَ ڢَاطَ ثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni, Damuwa ta fi ƙarfina. Sun yi wushefe a kan hanyata, Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.