Psalms 59:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيْ، يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ مَيْ ضُنْدُنَا، كَيْنٜىٰ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ تَاشِ كَحُكُنْتَ دُكَنْ أَلْعُمَّيْ، كَدَ كَنُونَ جِنْڧَيْ غَ مَاسُثِنْ أَمَانَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni, Ka tashi ka hukunta al'ummai, Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!