Psalms 62:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كُدُواْغَرَ غَ عَيْكِنْ ثُوتَا، كُواْ كُسَا رَيْ غَ ثِنْ رِيبَ دَغَ عَيْكِنْ ڢَشِ؞ كُواْ دَ أَرْزِڧِنْكُ يَڧَارُ، كَدَ كُدُواْغَرَ غَرٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta ƙaru, Kada ku dogara gare ta.