Psalms 65:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَنَ كُلَ دَ ڧَسَا تَوُرِنْ بَاتَ ضُوً سَمَ، كَسَا تَبَادَ أَمْڢَانِ مَيْ يَوَ، كُواْغُنَنْ اللَّهْ سُنْثِكَ دَ ضُوَ، دُواْمِنْ سُبَا مُتَنٜىٰ حَڟِ؞ غَمَا حَكَ كَشِرْيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kakan nuna kana kulawa da ƙasar, Ta wurin aiko mata da ruwa. Ka arzuta ta, ta zama dausayi. Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba, Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki, Abubuwan da ka aikata ke nan.