Psalms 68:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڟَاوَتَا وَ أَلْعُمَّ مَيْ غَابَادَمُو، وَنَّنْ دَبَّ مَيْ ٻُواْيٜىٰوَ عَثِيَوَ تَبَاكِنْ كُواْغِ؞ ڟَاوَتَا وَغَرْكٜىٰنْ بِجِمَنَّنْ مَيْ ذَمَ عَثِكِنْ یَیَنْ شَانُو، حَرْ سَيْ سُنْ ذُواْ غَبَنْكَ دَ ضَوَرْ جِكِے سُنَ مِيڧَ مَكَ كُطِنْ أَظُرْڢَا؞ وَاڟَرْ دَ ڧَبِيلُ مَاسُسُوانْ يِنْ يَاڧِ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka tsauta wa Masar, naman jejin nan Mai zafin hali da yake cikin iwa, Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu, Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu. Ka warwatsar da jama'ar nan Masu son yin yaƙi!