Psalms 69:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ سَا ذُوثِيَا غَرٜىٰكَ سُشَا كُنْيَا سَبُواْدَنِ، يَا عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ؞ كَدَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ نٜىٰمَنْكَ عَثِ مُتُنْثِنْسُ سَبُواْدَنِ، يَا اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka, Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka! Kada ka bar ni in jawo abin kunya Ga waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!