Psalms 78:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَامُ ٻُواْيٜىٰوَ یَیَنْمُبَ، ذَامُ ڢَطَا وَاڟَارَ مَيْ ذُوَا أَيُّكَنْ يَهْوٜىٰهْ دَ سُكَ إِسَ يَبُواْ دَ كُمَ ڧَرْڢِنْسَ، تَرٜىٰدَ أَيُّكَنْ بَنْ مَامَاكِنْ دَ يَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba, Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwa Labarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa, Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.