Psalms 78:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ كَدَ سُذَمَ كَمَرْ كَاكَنِّنْسُ مَاسُ تَوْرِنْ كَيْ، مَاسُ يِنْ تَاوَيٜىٰ، ڟَارَرْ دَ ذُوثِيَارْسُ بَسُ كَڢُ دَرَمْبَ، أَ رَنْسُ بَسُيِ أَمِنْثِ غَ اللَّهْ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada su zama kamar kakanninsu, Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya. Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba, Ba su kuwa yi masa aminci ba.