Revelation 1:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڟَكِيَرْ سَنْدُنَ مَاسُ رِڧٜىٰ ڢِتِلُنَّنْ كُوَ نَغَ وَنِ مَيْ كَمَنِّنْ طَنْ مُتُمْ يَنَ سَنْيٜىٰ دَ دُواْغُوَرْ رِغَا، ڧِرْجِنْسَ كُمَ دَ طَمَرَرْ ظِينَارِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A tsakiyar fitilun nan kuwa, na ga wani kamar Ɗan Mutum, saye da riga har idon sawu, ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya.