Revelation 1:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ حَنُّنْ دَامَرْسَ يَنَ رِڧٜىٰ دَ تَوْرَرِ بَݣَويْ دَغَ بَاكِنْسَ كُمَ تَكُواْبِے مَيْ بَاكِ بِيُ مَيْثِ سُواْسَيْ يَنَ ڢِتُواْوَ؞ ڢُسْكَرْسَ تَنَ حَصْكٜىٰ كَمَرْ رَانَ أَڟَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama, daga bakinsa kuma takobi mai kaifi biyu yake fitowa. Fuskarsa tana haske kamar rana a tsaka.