Revelation 10:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْنَتَڢِے وُرِنْ مَلاَىِٕكَنْ نَثٜىٰمَسَ يَبَانِ ڧَرَمِنْ لِتَّڢِنْ؞ شِے كُوَ يَثٜىٰمِنِ «كَكَرْٻَ كَثِ، ذَيْ ذَمَ دَ طَاثِ عَثِكِنْكَ، عَمَّا عَبَاكِنْكَ ذَيْ ذَمَ دَ ذَاڧِ كَمَرْ ظُمَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”