Revelation 11:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْعُمَّيْ سُكَ ثِكَ دَ ڢُشِے، عَمَّا يَنْذُ لُواْكَثِنْ ڢُشِنْكَ يَا ذُواْ، لُواْكَثِ يَيِ دَ ذَاعَيِ وَمَتَتُّو شَرِيعَ، ذَاعَ بَادَ لَادَ غَ بَايِنْكَ أَنَّبَاوَا، دَ ڟَرْكَكَا وَطَنْدَ سُكٜىٰجِنْ ڟُواْرُوانْ سُونَنْكَ، دَ مَنْيَ دَ ڧَنَانَا؞ لُواْكَثِ يَيِ دَ ذَاعَ هَلَّكَ مَاسُ هَلَّكَ دُونِيَا!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Al'ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko, Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari'a, A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba, A kuma hallaka masu hallaka duniya.”