Revelation 11:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاعَبَرْ غَوَوَّكِنْسُ عَكَنْ تِيتِنْ بَبَّنْ بِرْنِنَّنْ دَ عَكَ غِثِّيٜىٰ عُبَنْ‌غِجِنْسُ ؞ أَنَ ݣُوتَنْتَا بِرْنِنَّنْ دَ سُونَ «سُواْدُوامْ» كُواْ «مَصَرْ»؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.