Revelation 12:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دُواْدُوانْ يَيِ ڢُشِے دَ مَثٜىٰنْ ڨُورَيْ، يَتَاسُواْ يَيِ ڢَطَ دَ سَوْرَنْ ذُرِيَرْ مَثٜىٰنْ، وَتُواْ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ كِيَايٜىٰ دُواْكُواْكِنْ اللَّهْ ، سُنَ كُمَ رِڧٜىٰ دَ شَيْدَرْ عِيسَىٰ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.