Revelation 14:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً وَنِ مَلاَىِٕكَ حَرْ يَنْذُ، وَنْدَ يَكٜىٰ لُورَ دَ وُتَرْ بَغَدٜىٰنْ يَڢِتُواْ دَغَ بَغَدٜىٰنْ؞ دَ بَبَّرْ مُرْيَ يَيِ كِرَا وَ وَنْثَنْ مَلاَىِٕكَ مَيْ لَوْجٜىٰ، يَثٜىٰ مَسَ، «مِيڧَ لَوْجٜىٰنْكَ كَيَنْكَ ڧُنْشِنْ یَیَنْ إِنَبِنْ دَغَ غُواْنَرْ إِنَبِنْ دُونِيَا، غَمَا یَیَنْسَ سُنْ نُونَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma wani mala'ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala'ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.”