Revelation 14:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَجِ وَتَ مُرْيَ دَغَ سَمَ مَيْ ڧَارَ كَمَرْ ضُوَ مَيْ غُدُ، كَمَرْ ڟَاوَ مَيْ ڧَارَ سُواْسَيْ؞ مُرْيَرْدَ نَجِ كُوَ كَمَرْ تَمَاسُ كِطِنْ مُواْلُواْ ثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na ji wata murya daga Sama kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, muryar da na ji kuwa, kamar ta masu molo ce na kiɗan molo.