Revelation 14:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنَ رٜىٰرَ وَتَ سَابُوَرْ وَاڧَا أَغَبَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ، أَغَبَنْ حَلِتُّو مَاسُ رَيْ غُدَا حُطُنَّنْ دَ كُمَ أَغَبَنْ دَتَّاوَنْ؞ بَابُوَنِ دَ ذَيْ عِيَ يَكُواْيِ وَنَّنْ وَاڧَا سَيْ مُتَنٜىٰ دُبُو طَرِے دَ دُبُو أَرْبَعِنْ دَ حُطُ طِنَّنْ كَوَيْ، وَطَنْدَ عَكَ ڢَنْشٜىٰسُ دَغَ دُونِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya.