Revelation 14:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ مُتَنٜىٰنٜىٰ وَطَنْدَ بَسُ تَٻَ ڧَظَنْتَرْدَ كَنْسُ تَوُرِنْ ݣُونَ دَ مَاتَا بَ، دُواْمِنْ سُنْيِ ذَمَنْ ڟَبْتَ؞ سُونٜىٰ سُكٜىٰبِنْ طَنْ ضَغُوانْ دُكْ عِنْدَ يَتَڢِے؞ وَطَنَّنْ نٜىٰ أَنْڢَنْشٜىٰسُ دَغَ ثِكِنْ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰ، سُونٜىٰ كُمَ كَمَرْ نُونً ڢَارِ نَأَمْڢَانِنْ غُواْنَرْ دَ ذَاعَ مِيڧَ غَ اللَّهْ دَ كُمَ طَنْ ضَغُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,