Revelation 15:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَلاَىِٕكُ بَݣَويْ مَاسُ بَلَعِ بَݣَويْ نَنْ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ ثِكِنْ هَيْكَلِنْ، سَنْيٜىٰ دَ رِيغُنَنْ لِيلِنْ مَيْ ڟَبْتَ مَيْ حَصْكٜىٰ دَ كُمَ طَمَرَرْ ظِينَارِيَ عَڧِرْجِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mala'ika bakwai ɗin nan masu bala'i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.