Revelation 15:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هَيْكَلِنْ يَثِكَ دَ هَيَاڧِنْ دَيَكٜىٰ ڢِتُواْوَ دَغَ طَوْكَكَرْ اللَّهْ دَ إِيكُوانْسَ؞ بَابُ كُوَ وَنِنْ دَ يَ عِيَ شِغَ ثِكِنْ هَيْكَلِنَّنْ سَيْ دَ بَلَعِنَّنْ بَݣَويْ نَمَلاَىِٕكُ بَݣَويْ طِنَّنْ سُكَ ڧَارٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala'i bakwai na mala'ikun nan bakwai sun ƙare.