Revelation 16:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْنَجِ وَتَ بَبَّرْ مُرْيَ تَنَ مَغَنَ دَغَ هَيْكَلِنْ، تَنَ غَيَ وَمَلاَىِٕكُ بَݣَويْ طِنَّنْ ثٜىٰوَ «كُتَڢِے كُجُويٜىٰ وَدُونِيَا وَطَنَّنْ ݣُونُواْنِ بَݣَويْ نَڢُشِنْ اللَّهْ ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala'ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”