Revelation 16:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عَكَيِ وَلْڧِيَ دَ ڧَرَرَّكِ دَ ڟَاوَ دَ كُمَ بَبَّرْ ضَوَرْ ڧَسَا إِرِ وَدَّ بَعَتَٻَيِبَ تُنْ حَلِتَّرْ مُتُمْ؞ بَبَّرْ ضَوَرْ ڧَسَاثٜىٰ ڨُورَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.